Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Santa Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da masu neman kujerar Shugaban Kasa a jam’iyyun APC da Kuma PDP.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne, a ranar Lahadi a garin Ado-Ekiti da ke a jihar Ekiti a yayin da ya je garin domin yin tuntuba kan takararsa.
- An Kama Wani Mutum Da Kullin Hodar Ibilis A Al’aurarsa A Legas
- Na Yi Babban Kuskuren Zabar Atiku Mataimakina A 1999 – Obasanjo
A cewarsa, dukkan jam’iyyun biyu sun gaza wajen samarwa da daukacin saukin kuncin rayuwa a fannoni da dama, inda ya kara da cewa, kayan masarafi a kullum sai kara hauhauwa suke yi a kasar nan.
Ya kara da cewa, lamarin rashin tsaro a daukacin fadin kasar nan na tabarbarewa, tsarin tattalin arizkinta ya janyo talauci, rashin aikin yi da hauhawan farashin kayan masarufi, inda ya yi nuni da cewa wadannan kawai, sun isa ‘yan kasar su yi watsi da zabar APC da PDP a zaben 2023.
Ya ci gaba da cewa, Nijeriya a yanzu na tunkarar babbar annoba, inda ya bayyana cewa, babu wani aiki kirki da ‘yan Nijeria za su sake samu daga gun jam’iyyun biyu domin babu wani abun azo a gani da suka yi.
Kwankwaso ya kuma koka kan yadda matafiya ke shan bakar wahala a kan babbar hanyar Akure zuwa garin Ado, inda ya ce APC mai mulki da gwamnatin jihar, sun yi watsi da hanyar ne don jefa masu binta a cikin wahala.