Jam’iyyar NNPP ta sanar da Barista Ladipo Johnson a matsayin mataimakin dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, a zaben 2023.
Johnson haifafen jihar Legas da ke Kudancin Nijeriya, ya taba neman kujerar gwamnan Jihar.
- Jam’iyyar LP Ta Obi Na Shirin Kulla Auren Siyasa Da NNPP Ta Kwankwaso —Dakta Tanko
- ‘Kwankwaso Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023’ —Jideogu Ogbu
NNPP ta wallafa a shafinta na Tuwita
@nnpphqabuja1, kuma sakataren watsa labarai na jam’iyyar, Major Agbor ya tabbatar da labarin.
Jam’iyyar ta rubuta cewa: “Domin tunkarar zaben 2023: Barista Ladipo Johnson shi ne mataimakin dan Shugaban Kasa na jam’iyyarmu.”
Jaridar LEADERSHIP ta ranar Juma’a ta wallafa cikin labaranta cewa an tantance mutum uku daga kudancin kasar nan da zimmar zabar mutum guda daga cikinsu da zai dafawa Kwankwaso a takara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp