Yayin da saura kasa da watanni biyu a fara zaben 2023, a ranar Lahadi, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kan ikirarinsa na ‘Emi Lokan’ (lokacina ne).
Obasanjo ya kara da cewa, irin wannan ba hali ne da ya dace ba ga mai neman shugabancin Nijeriya.
Tsohon shugaban kasar, wanda ya caccaki Tinubu a wata budaddiyar wasika da ya aikewa ‘yan Nijeriya a ranar bikin sabuwar shekara, ya bukaci matasan Nijeriya da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, a matsayin shugaban kasar Nijeriya a 2023.
“Bari na fada kai tsaye ‘Emi Lokan’ da ‘Na sauke nauyin dake kaina’ abu daya ne kuma ba daidai ba ne dan takarar shugabancin Nijeriya a yanzu ya fada haka, ma’ana ba zai iya farfado da kasar ba ballantana kafa sabuwar kasa da zata hade kan ‘yan Nijeriya.