• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2023: Za A Bai Wa ‘Yan Hijira Damar Kaɗa Kuri’a A Sansanoninsu – INEC

by Sulaiman
3 years ago
INEC

A ƙoƙarin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke yi don ganin ta yi shirin gudanar da zaɓen 2023 da wuri, Shugaban IINEC Farfsa Mahmood Yakubu ya jaddada cewa aƙalla fiye da ‘yan gudun hijira milyan uku ne za su yi zaɓe a sansanoni daban-daban a ƙasar nan.

Yakubu ya ƙara da cewa tuni hukumar sa ta fara aikin tsame sunayen waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko fiye da haka.

  • 2023: Ba Da Jimawa Ba Za Mu Wallafa Cikakken Sunayen Wadanda Aka Yi Wa Rajistar Katin Zabe – INEC

Shugaban na INEC ya bayyana fara aikin tsame sunayen waɗanda su ka yi rajistar Mallakar katin zaɓe sau biyu ko fiye da haka cikin wannan makon a Abuja.

Ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi a wurin taron masu ruwa da tsaki, kan bitar fayyace ƙa’idojin zaɓe a sansanin masu gudun hijira, wanda aka shirya ranar Talata, a Abuja.

An shirya taron ne ranar Talata a Abuja, inda Yakubu ya ce sake nazarin tsare-tsaren ya zama wajibi, domin rabon da a sake bibiyar sa tun na ƙarshe da aka yi a 2018, kafin zaɓen 2019.

LABARAI MASU NASABA

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

Ya ce ana nan ana kuma ci gaba da tsame sunayen da aka yi rajista sau biyu ko fiye da haka ana zubarwa, domin a tabbatar da cikakkun adadin yawan waɗanda za su mallaki katin rajistar zaɓe guda ɗaya tilo, kamar yadda doka ta tanadar.

Ya ce sai an kammala tsame sunayen masu rajistar fiye da sau ɗaya sannan za a bayyana ranar da za a liƙa sunayen masu rajista, kowa ya gani a faɗin ƙasar nan.

“A tsarin ganin an gudanar da zaɓuka cikin sansanin ‘yan gudun hijira, mu na so mu tabbatar cewa wannan tsari kamar yadda doka ta tanadar, ba a bar kowa a baya ba.

“Za mu tabbatar kamar yadda dokar zaɓe ta shimfiɗa cewa an gudanar da zaɓe a sansanin masu gudun hijira, kuma naƙasassu sun samu damar yin zaɓe da kuma waɗanda wani Ibtila’i na barin gidajen su ya shafe su, kamar ambaliya.”

Yakubu ya ce aƙalla akwai mutane miliyan uku a sansanonin gudun hijira daban-daban a ƙasar nan.

Ya ce taron sake nazarin su ya zama wajibi a yanzu, saboda masu gudun hijira ɗin sun ƙaru, sakamakon wasu dalilai, kamar ambaliya.

Ya ce a yanzu kuma za a bayar da himma wajen ganin an wayar da kan mazauna sansanonin gudun hijira dangane da muhimmancin zaɓe da kuma ƙa’idojin da doka ta shimfiɗa wajen gudanar da zaɓe a cikin masu gudun hijira.

Shugaban INEC ya musanta zargin da Gamayyar Ƙungiyoyin Kare Haƙƙin Jama’a (CSO) su ka yi wa INEC cewa ta karya dokar Sashe na 19(1) na Dokar Zaɓe, sashen da ya fayyace yadda INEC za ta liƙa sunayen waɗanda su ka yi rajista, domin kowa ya gani a ƙasar nan.

“Ba mu karya wata doka ba. Saboda har yanzu ana kan tantancewa da tsame sunayen waɗanda su ka yi rajista sau biyu ko fiye da biyu tukunna. Idan lokacin da za mu liƙa sunayen ya yi, za mu sanar kowa ya sani, kuma ya gani.” Inji Yakubu.

Ya ce za a liƙa sunayen a dukkan mazaɓu 8,809 da ake da su a ƙasar nan a dukkan ƙananan hukimomi 774 a Nijeriya, kamar yadda Sashe na 19(1) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar.

Ya ce za a haɗa sunayen da aka yi rajista a baya-bayan nan tare da adadin miliyan 84 da ake da su a baya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
Manyan Labarai

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi
Manyan Labarai

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal
Labarai

Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

November 8, 2025
Next Post
Hajjin 2022: Gwamnatin Zamfara Ta Mayar Wa Alhazai 1,318 Naira 50,000 Kowanne

Hajjin 2022: Gwamnatin Zamfara Ta Mayar Wa Alhazai 1,318 Naira 50,000 Kowanne

LABARAI MASU NASABA

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025
Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE

November 8, 2025
Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

Lalacewar Tarbiyar Dalibai Mata A Makarantun Islamiyya Da Na Boko

November 8, 2025
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya

November 8, 2025
Yadda Ake Miyar Margi

Yadda Ake Miyar Margi

November 8, 2025
Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi

November 8, 2025
Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal

November 8, 2025
Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10

November 8, 2025
Maganin Nankarwa (4)

Maganin Nankarwa (4)

November 8, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

Kotu Ta Yanke Wa Wata Budurwa Hukuncin Shekaru 4 A Kano, Duba Laifinta

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.