Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kasance ma su goyon baya da ci gaba da yin addu’o’i don ganin an samu cikar shirin “sabuntawa” na Shugaba Bola Tinubu.
Wannan yana bunshe ne a cikin sakon sabuwar shekara ga al’ummar jihar Kebbi da ‘yan Nijeriya nagari da gwamnan ya gabatar, ya kuma bayyana fatansa na alheri ga sababbin kudurorin gwamnatin Tinubu a matsayin hanyar sake fasalin kasa da kawo sauyi domin amfanin kowa.
- Karin Albashi: Ma’aikatan Nijeriya Za Su Dara a 2024 – Tinubu
- Ba Za Mu Lamunci Lalaci Daga Waɗanda Aka Naɗa Muƙamai Ba– Tinubu
“Ina so na karfafawa ‘yan Nijeriya guiwa da su kasance masu da’a da ci gaba da yin addu’a ga shugaban kasa don ya samu ya tabbatar da burinsa na sabuntawa. Da Wannan na yi imani zai canza kasar zuwa ga manufa mai kyau.
Hakazalika “Ina kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su goyi bayan manufofi da shirye-shiryen jam’iyyar APC a dukkan matakai don bai wa wadanda ke kan madafun iko damar samar da riba a tafarkin dimokuradiyya ga kowa,” in ji shi.
Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar jihar Kebbi cewa ba zai huta ba har sai ya kawo canjin da ake so a jihar baki daya, don haka akwai bukatar goyon bayan jama’a daga bangarori daban-daban na jihar..