A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da matakin biyan albashin wata na 13 a wata takardar da shugaban ma’aikata Ahmed Aliyu Liman ya sanya wa hannu.
Sanarwar da Kakakin Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce, biyan irin wannan karin albashi na watanni 13 shi ne irinsa na farko a tarihin Jihar.
A cewarsa, matakin ya yi daidai da kudurin gwamnatin jihar na kyautata jin dadin ma’aikata da kuma zaburar da ma’aikata wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp