Jami’in ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, jari da kasar Sin ta zuba a ketare da hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen waje sun samu ci gaba bisa daidaito a shekarar 2024.
A cewar jami’in, a bara, jarin kai tsaye na Sin a kasashen waje wanda ba na tsabar kudi ba ya karu da kashi 10.5 cikin dari bisa na shekarar 2023 zuwa dalar Amurka biliyan 143.85, inda jarin da ta zuba a kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya (ASEAN) ya karu da kashi 12.6 cikin dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2023.
- Gwmana Lawal Ya Bayyana Wa UNICEF Shirin Jihar Zamfara Na Ƙaddamar Da Dokar Kare Al’umma
- Shugaban Kasar Sin Ya Mika Gaisuwar Sabuwar Shekara Ga Dukkan Jami’an Tsaro
Haka zalika, jari a harkokin da suka shafi haya, hidimar kasuwanci, masana’antu, da fannin dillalai da masu sari duk sun ingiza karuwar. Jami’in ya kara da cewa, yawan darajar ayyukan da kasar Sin ta yi kwangilarsu a kasashen waje ya kai dalar Amurka biliyan 165.97 a shekarar 2024, wanda ya karu da kashi 3.1 cikin dari bisa na shekarar 2023.
Har ila yau, a shekarar 2024, adadin ma’aikatan da Sin ta aika zuwa kasashen waje ya kai 409,000, adadin da ya karu da kashi 17.9 cikin dari bisa na shekarar 2023, inda a karshen shekarar ta 2024 adadin ma’aikatan kasar Sin da suka yi aiki a kasashen ketare ya kai 594,000.
Jarin kai tsaye na Sin a a kasashen da ke aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya wanda ba na tsabar kudi ba ya karu da kashi 5.4 cikin dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2023, zuwa dalar Amurka biliyan 33.69 a bara, a cewar bayanan ma’aikatar. (Mohammed Yahaya)