Tsohon mashawarcin shugaban kasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya hakura da shirin neman tazarce, ya bai wa matasa dama su yi takara domin ciyar da kasa gaba a babban zabe na 2027.
A wata budaddiyar wasika da ya aike wa Daily Trust a ranar Laraba, Baba-Ahmed ya roki Tinubu da ya yi watsi da duk wani shirin sake tsayawa takara a 2027.
- Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Minista
- Dalilin Da Zai Iya Hana Ni Sake Bugawa Manchester United Wasa – Rashford
Baba-Ahmed ya bayar da hujjar cewa, Tinubu ya ajiye son ransa, ya bar matasa a mulki, ya fice daga Siyasa a mutunce, shi ne dattaku da barin baya da kyau.
“Ka koma gefe – ba wai kabar wa abokan hamayyarka takara ba, amma don sabbin jini matasa ‘yan Nijeriya da za su iya ciyar da al’umma gaba da sabbin kuzari da tunani.” in ji shi.
Ya kara da cewa, ya kamata shugaban kasa ya yi tunani a kan nagartattun abubuwan da yake son bari bayanshi da kuma yadda tarihi zai tuna da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp