Ganawar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ta haifar da cece-kuce a harkokin siyasa.
A karshen mako ne tsohon gwamnan Jihar Osun, Aregbesola, ya karbi bakoncin, tsohon gwamnan Jihar Kano, Kwankwaso a gidansa da ke Legas.
- Kwankwaso Ya Soki Ƴansandan Kano, Ya Buƙaci A Girmama Ƴancin Kano
- Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya
‘Yan siyasar sun gana ne a daidai lokacin da jiga-jigan ‘yan adawa ke laluban hanyoyin da za su bi domin kwace mulki a hannun Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a zaben 2027.
Ganawar ta zo ne kwanaki kadan bayan da Aregbesola da magoya bayansa suka fice daga APC a Osun. Sun yi ikirarin cewa sun fice daga APC ne saboda yadda shugabannin jam’iyyar ba sa musu adalci da kuma ci gaba da tozarta tsarin jam’iyyar.
APC ta kori Aregbesola daga jam’iyyar bisa zargin cin zarafin jam’iyyar. Masu fashin baki na danganta hakan da dalilin ganawar da Aregbesola ya yi da Kwankwaso wanda ya janyo rade-radin cewa yiwuwar ‘yan siyasar biyu su yi aiki tare kafin 2027.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ita ma ta shiga cikin rikici, inda ake zargin Kwankwaso ne ke jagorantar daya daga cikin bangarorin jam’iyyar.
A makon da ya gabata ne wani bangare na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin wanda ya assasa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam ya gudanar da babban taro a Legas, inda aka zabi sabbin mambobin kwamitin zartarwa na kasa.
Kwankwaso ya tabbatar da ganawarsa da Aregbesola a wani sako da ya fitar. Ya ce, “A yammacin yau na yi farin cikin ziyartar tsohon gwamnan Jihar Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a gidansa da ke Legas. Taron ya ba mu damar tattaunawa a kan harkokin siyasar kasar nan da gudanar da mulki da kuma makomar dimokuradiyyar Nijeriya.”
Wata majiya mai tushe ta ce, “Taron ya ta’allaka ne kan yadda ‘yan siyasar biyu suka tsara dabarun makomarsu duba da irin matsalar da suke fuskanta a jam’iyyunsu. Don haka, zan iya cewa sun tattauna komai game da zaben 2027 ne.”
Wata majiya a bangaren Aregbesola ta bayyana cewa ‘yan siyasar biyu suna auna zabi hanyoyi daban-daban kafin 2027 kuma ana ci gaba da tattaunawa.