Kwamishinan ‘yansandan jihar Abia, Mista Kenechuchu Onwuemelie, ya ce, rundunar za ta shiga ta fita ta kawo fasahohin zamani domin kara himma wajen kyautata harkokin tsaro a jihar.
Onwuemelie ya shaida hakan ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida bayan kammala ganawar tsaro a Nbosi da ke karamar hukumar Isiala ta Kudu.
- Rundunar ‘Yansanda Ta Shelanta Neman Dakta Idris Dutsen Tanshi Ruwa A Jallo
- Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Kwamitin Asusun Samar Da Tallafin Tsaro
Ya ce, matakin wani bangare ne na kokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen ganin an kyautata da magance matsalolin tsaro a jihar Abia.
“A ‘yan kwanakin nan, zai yi wuya ka ga an aikata wani laifi a halin yanzu ba tare da an yi amfani da wani nau’in fasaha ba, don haka, ta hanyoyin fasahar da ake bi wajen aikata laifukan, ta hanyoyin ya dace a bi wajen dakile ta’addanci da ‘yan ta’adda.
“Don haka, a cikin hanyoyi da matakan da ake dauka na kyautata tsaro, akwai batun amfani da fasahar zamani da na’urorin zamani.
“Tun kafin yanzu jihar ta sanya nau’ororin daukan hoton CCTB a wasu muhimman wurare kuma ana cigaba da kara Sanya su a wasu wuraren da suka dace.
“Akwai bukatar mu kara inganta hanyoyin sadarwa, sannan akwai gayar muhimmancin kara kyautata hanyoyin bada rahoto ta hanyar kiran kar-ta-kwana domin shigar da rahotonni,” shugaban ‘yansandan ya shaida.
Ya daura da cewa rungumar hanyoyin fasahar zamani za su taimaka sosai wajen inganta lamuran tsaro da dakile ayyukan ‘yan ta’adda.
A cewar sa, hukumomin tsaro, gayar bukatar sadarwa cikin gaggawa wanda ta hakan ne za su samu damar dakile duk wata yunkurin tafka ta’asar bata gari.