Daga ranar 24 ga wata, zuwa jiya Asabar 26 ga wata, an gudanar da babban taron kasa da kasa, dangane da fasahar rage asarar hatsi a birnin Jinan na kasar Sin, inda a wajen taron aka sanar da sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin takaita asarar hatsi.
An bayyana cewa, a bangaren asarar hatsi da a kan samu yayin da ake girbin hatsi da injuna, yawan asarar alkama, da shinkafa, da masara, da aka samu a kasar Sin a shekarar 2024, ya kai kaso 0.93%, da 1.76%, da kuma 2.06%, adadin da ya ragu da kaso 1% zuwa kaso 2%, bisa na shekarar 2021, ta yadda aka magance asarar hatsin da yawansa ya kai kilo biliyan 25 cikin shekaru 3 da suka gabata.
Kana ta fuskar tinkarar bala’i, da magance tafka hasara sakamakon hakan, kasar Sin ta riga ta gina ingatattun filayen gona da fadinsu ya kai muraba’in kilomita dubu 667. Kana kasar ta dauki gagarumin mataki na haka magudanar ruwa cikin gonaki, ta yadda aka tabbatar da ingancin aikin ban ruwa, da fitar da ruwa a lokacin ambaliya, a cikin fiye da rabin gonakin kasar. Ban da haka, kasar ta karfafa yin gargadin yiwuwar abkuwar cututtukan da suka shafi hatsi, da bala’in kwari, ta yadda ake samu damar rage asarar hatsi da yawansa ya kai fiye da kilo biliyan 140 a duk shekara. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp