Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin ya karrama ƴan wasan Super Falcons bayan nasarar da suka samu a gasar ‘2024 Women’s Africa Cup of Nations (WAFCON) da aka gudanar a Maroko.
A lokacin da ya tarɓe su a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Tinubu ya ba kowacce daga cikin ƴan wasa 24 lambar girmamawa ta Officer of the Order of the Niger (OON), tare da kyautar gida mai dakuna uku da kuma Dala 100,000 kowacce.
- Super Falcons Sun Iso Abuja Ɗauke Da Kofin WAFCON
- Kwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Ethiopia Da Ci 4 A Abuja
Ya kuma bai wa kowane ɗan kwamitin fasaha (technical crew) kyautar $50,000, tare da yabawa dabarun da suka yi amfani da su wajen dawo da wasan daga kwallo 2 ana jefa su zuwa lashe 3-2 a kan Maroko a Rabat.
“Ina taya ku murna. Kun ɗaga darajar Nijeriya. Kun tabbatar cewa Nijeriya ba za a dakushe ta ba idan muka haɗu wuri guda,” in ji Tinubu. “Jarumta, ƙwazo da haɗin kan ku ya zame wa ƙasar nan abin alfahari.”
Matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu da matar mataimakin shugaban ƙasa, Nana Shettima, sun halarci taron bikin girmamawar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp