A shekarar bara kasar Sin ta ci gaba da bunkasa amfani da fasahohin dijital, a sassan samar da hidimomi daban daban ga al’ummar kasar, ciki har da fannin jinya, da kiwon lafiya, da tsaro, da samar da ayyukan yi da kula da tsofaffi, matakin da ya kara samar da zarafi na inganta rayuwar al’umma, kamar dai yadda wani sabon rahoto da aka fitar game da hakan ya nuna.
Yayin fitar da rahoton na kwanan nan, jami’i a hukumar kasar Sin mai lura da hidimomin intanet Wen Ruisong, ya ce ya zuwa karshen shekarar 2024 da ta gabata, adadin al’ummar Sin da ke amfani da hidimomin intanet a fannin kiwon lafiya ya kai mutum miliyan 418, yayin da adadin ‘yan kasar da ke da katin dijital na samar da hidimomin al’umma na kasa ya kai mutum biliyan 1.07.
Wen ya kara da cewa a duk tsawon shekarar ta bara, mahukuntan kasar Sin sun ci gaba da kyautata dukkanin damammakin cin gajiyar hidimomin dijital ga al’ummar Sin. Ya ce karkashin wannan kwazo, Sin ta cimma manyan nasarori a fannin gina tsarin tattara manyan bayanai na kashin kai, da bunkasa shigar da hidimomin da gwamnati ke samarwa jama’a cikin tsarin dijital mai inganci. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp