Shugaban ƙungiyar Jihohin Arewa, Gwamnan Jihar Gwambe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa; Shugaba Bola Tinubu, ya cika alƙawuran da ya ɗauka a 2023, sannan kuma har yanzu yana kan ci gaba da cika su.
Gwamna Yahaya, ya bayyana haka ne a taron tattaunawa na kwana biyu da aka gudanar, kan haɗin gwiwar gwamnati da jama’a, wanda Gidauniya Ahmadu Bello (SABMF), ta shirya a Arewa House da ke Kaduna.
ɗa yake jawabi a kan taken taron, “Tantance Alƙawarukan Zaɓe: ƙarfafa Haɗin Gwiwar Gwamnati da Jama’a ɗon Haɗin Kan ƙasa”, Gwamna Yahaya ya ce; yana magana ne a kana bin da ke sa demokuraɗiyya ta kasance mai ma’ana.
“Sakamakon wannan haɗuwa da muka yi da wakilan gwamnatin tarayya, wajibi ne mu farad a yin adalci da kuma abin da ya dace. Haɗin gwiwar Arewa da Gwamnatin Shugaba Tinubu, ya yi matuƙar haifar da sakamako mai kyau, kama daga samun ayyukan more rayuwa zuwa batun samar da tsaro.
“A 2027, dole ne a rama wa kura aniyarta, ta hanyar bai wa Shugaba Tinuba cikakken haɗin kai wajen ci gaba da mulki a faɗin wannan ƙasa,” in ji shi.
Gwamnan Jihar ta Gwambe, ya tunatar da cewa; a lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a gabanmu a matsayin ɗan takara a yaƙin zaɓen 2023, ya yi wa Arewacin Nijeriya alƙawura na musamman. Kazalika, Arewa ta amince da manufofin shugaban ƙasar, ta kuma yi tsayin daka wajen zaɓensa, inda suka bayar da gudunmawa na kimanin kashi 60 cikin 100 na ƙuri’un da Tinubun ya samu.
“A yau, ga shi mun taru, domin yin nazari a kan waɗancan alƙawuran tare kuma da tantance irin ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, abubuwan da muka samu su ne; sauye-sauyen da aka samu duk kuwa da irin ƙalubalen da ake fuskanta a wannan ƙasa. Wannan na nuna cewa, demokuraɗiyyarmu za ta iya yin aiki ne kaɗai idan ana cika alƙawuran da aka ɗauka, sannan shugabanni ba za su iya aiwatar da alƙawuran ba har sai sun samu haɗin kan ƴan ƙasa.
“Zan iya bugun ƙirji wajen bayyana irin ci gaban da yankinmu na Arewa ya samu. ɗon haka, muna yi wa shugaban ƙasa godiya dangane da waɗannan sabbin tsare-tsaren ci gaba da ya kawo mana, mafi yawan ayyukan day a gada daga gwamnatin da ta gabata, yanzu haka yana kan hanyar kammala su.”
Ya bayyana ire-iren waɗannan ayyuka da suka haɗa da aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano, layin jirgin ƙasa na Kano zuwa Katsina zuwa Maraɗi, gyaran matatar mai ta Kaduna, aikin bututun iskar gas na Abuja, Kaduna, Kano da kuma ci gaba da aikin haƙar mai a Kolmani.
“Waɗannan ayyuka, ko shakka babu; za su kawo ci gaba a ɓangaren masana’antu da samar da tsaro a yankunanmu na Arewa,” in ji shi.
Gwamna Yahaya ya ƙara da cewa, akwai kuma wasu sabbin ayyukan more rayuwar da ken an tafe, waɗanda suka haɗa da hanyoyi daban-daban a tsakanin jihohi kamar babbar hanyar Sakkwato zuwa Badagiri, wadda za ta haɗa ƴan kasuwar Arewa da na Kudu da kuma shirin samar da harkokin nomad a zai shafi Arewa.
Bugu da ƙari, ya lissafo wasu da suka haɗa da faɗaɗawa tare da inganta cibiyoyin harkokin kiwon lafiya, wanda y ace; dukkanninsu suna nuni ga manufar da aka tsara, don inganta rayuwar al’ummar wannan yanki na Arewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp