Sanata Shehu Buba Umar, mai wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattijai, ya ƙaddamar da rabon takin zamani tireloli bakwai ga manoma a mazaɓarsa domin ƙarfafa harkokin noma da tabbatar da wadatar abinci a yankin.
Wannan aiki na tallafa wa manoma ya zo ne a matsayin wani ɓangare na shirin ci gaba da ya sanya gaba tun farkon, wanda ya ce shi ne karo na uku da yake rabon irin wannan kayan tallafi ga manoma a shekara ta 2025.
- Shugaban Hukumar Zaɓe Ta Bauchi, Ahmad Makama, Ya Rasu
- Allah Ya Yi Wa Wakilin Sadarwan Bauchi, Jafaru Ilelah, Rasuwa
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin wani taron ƙaddamarwa da aka gudanar a ranar Lahadi, inda ya samu rakiyar shugabannin jam’iyyar APC da ƙungiyoyin manoma daga sassa daban-daban na mazaɓar.
Baya ga rabon takin, Sanatan ya ƙaddamar da shirin hujin shanu a ƙauyen Gwabiya, inda ya bayyana cewa sama da shanu 85,000 za su samu riga-kafi don kare lafiyarsu da inganta kiwo. Wannan na zuwa ne bayan wani irin shiri makamancin haka da aka gudanar a farkon shekara a ƙauyen Buzaye inda aka yi wa dabbobi 40,000 riga-kafi.
Sanatan ya yi kira ga kwamitin rabon taki da su tabbatar da gaskiya da adalci a yayin rabon kayan, inda ya nuna kwarin guiwa ga tsarin amma ya roƙi ƙara himma don tabbatar da cewa tallafin ya kai hannun kowa ba tare da nuna bambanci ba.
Wannan mataki yana daga cikin manyan matakan da za su tallafa wa inganta tsaron abinci, rage fatara, da ƙarfafa zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a Bauchi ta Kudu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp