Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta kwashe dukkan fursunoni daga gidan yari na Kurmawa wanda yake tun zamanin mulkin mallaka zuwa wani sabon gidan yari da aka gina a Janguza, inda za ta mayar da tsohon gidan yarin gidan tarihi.
Ibrahim Adam, mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai a tawagar gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar da hakan.
- Kashe N712bn Kan Gyaran Filin Jiragen Saman Legas Rashin Sanin Ya Kamata Ne – ADC
- Wani Babban Jigon APC Ya Fice Daga Jam’iyyar A Katsina
“Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta mayar da dukkanin fursunonin da ke gidan yarin Kurmawa a halin yanzu zuwa Janguza, yayin da za a mayar da gidan yarin na Kurmawa gidan tarihi da aka kebe domin adana kayayyakin tarihi da kuma bunkasa al’adun jihar.” In ji Adam.
Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi.
An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano.
Kano tana da gidan yari guda goma. Biyu a cikin birni—Kurmawa da Goron Dutse, yayin da sauran kuma suke a kananan hukumomin Wudil, Kiru, Rano, Sumaila, Bichi, Tudun-Wada, Gwarzo, da Dawakin-Tofa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp