Tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Wukari/Ibi ta jihar Taraba a majalisar wakilai, Hon. Shiddi Danjuma Usman ya fice daga jam’iyyar APC.
Usman ya bayyana rikicin cikin gida na jam’iyyar da rashin bin ka’idojin dimokuradiyya a matsayin dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara
- Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi
Shiddi, wanda ya wakilci mazabarsa a majalisar wakilai ta 8 da ta 9, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai a ranar Lahadi.
Tsohon dan majalisar ya ce, matakin da ya dauka na ficewa daga jam’iyya mai mulki ya biyo bayan tunani na tsawon watanni da kuma kara nuna damuwa game da abin da ya bayyana a matsayin ficewar jam’iyyar APC daga dabi’un da suka zaburar da shi tsunduma cikinta a baya.
Sai dai kuma, tsohon dan majalisar bai bayyana matsayinsa na siyasa na gaba ba duk da cewa an kada gangar zaben 2027 inda ‘yan adawa ke barazanar hambarar da jam’iyyar APC mai mulki daga mulki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp