Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya.
Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a majalisar masarautar Gudi.
- Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule
- Wasu Kungiyoyi Sun Yi Kira Ga Dan Majalisa Aminu Sani Jaji Ya Fito Takarar Gwamnan Zamfara
Kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya da fasaha na jihar, Farfesa Muhammad Bello Kawuwa ne ya mika takardar nadin ga sabon sarkin a madadin gwamnan.
Da yake isar da sakon Gwamnan, Farfesa Kawuwa ya bayyana muhimmiyar rawar da masarautar ke takawa wajen bunkasa ci gaban al’umma, magance rikice-rikice da kuma adana kayayyakin tarihi.
Ya bukaci sabon sarkin da ya gudanar da wadannan ayyuka cikin adalci, mutunci, da tsoron Allah.