Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da umarnin tattara ra’ayoyin jama’a masu amfani da kafar intanet yayin da ake tsara shirin raya kasa na shekaru 5-5 karo na 15, tsakanin 2025-2030.
Shirin raya kasa na shekaru 5-5 da Sin take yi, wani aiki ne na hangen nesa da zama cikin shiri da tsara tafarkin da za ta bi na cimma bunkasar tattalin arziki da kyautatuwar zamantakewar al’umma cikin shekaru 5-5.
Shin me umarnin tattara ra’ayoyin jama’ar intanet yake nunawa?
Na kan yi dariya idan na ji wasu na cewa akwai matsalolin take hakkin jama’a a kasar Sin, domin hakan na nuna cewa, ba su da masaniya kan ainihin yanayin da Sin take ciki ko kuma suna take gaskiya domin cikar wasu burikansu na boye. Kamar yadda hukumomin Sin kan bayyana a kullum, demokuradiyyar kasar ita ce, mai da hankali kan jama’a ta kowacce fuska, kuma ita ce demokuradiyyar da jama’a suke amfana da ita.
Wasu za su ce, to ta yaya za a tattara ra’ayoyin wadanda ba sa amfani da intanet?
Sadarwar intanet da lantarki da ruwa da sauran abubuwan bukatun jama’a na yau da kullum sun game baki dayan kasar Sin. Ni ganau ce ba jiyau ba, domin na yi tafiye-tafiye da dama, na shiga kauyukan kasar Sin, kuma cikinsu babu inda na ziyarta da ban ga wadannan abubuwa da na ambata ba.
Idan muka ajiye batun sadarwar intanet a gefe, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ita ce majalisar koli mai tsara dokoki a kasar, kuma wakilanta na fitowa ne daga dukkan bangarori da yankunan kasar. Sabanin yadda muka saba gani a kasashenmu inda wakilan jama’a ke tarewa a babban birnin, wakilan jama’a a kasar Sin na komawa ne cikin al’ummominsu, kuma a nan suke tattaro ra’ayoyi da shawarwari da bukatun jama’a.
Yayin da ake bin tsarin demokuradiyya, to ya zama wajibi walwala da kwanciyar hankalin jama’a su zama a kan gaba. Ina da yakinin yadda gwamnatin Sin ke sauraron ra’ayin jama’a da aiki tukuru wajen kyautata rayuwarsu na da nasaba da yadda jama’ar ke da kishin kasa da kokarin tallafawa ayyukan gwamnati. Tsarin demokuradiyyar kasar Sin ya nuna yadda gwamnati ke sauke nauyinta na hidimtawa jama’a da yadda jama’ar suke sauke nauyinsu na ba da gudunmawa ga ci gaban kasa da kishin kasa da kiyaye dokoki.
Hakika irin wannan tsari shi ake kira da ainihin demokuradiyya kuma irinsa ne ya dace da galibin kasashen duniya musamman masu tasowa dake kallon kasar Sin a matsayin a bar koyi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp