Shugaban rundunar adalci ta Jihar Sakkwato, Basharu Altine Guyawa Isa ya bayyana cewa gawurtaccen jagoran ‘yan ta’adda da ke hana wa al’umma bacci da idanu biyu, Bello Turji bai aminta da matakin sulhu da kowa ba.
Guyawa, wanda ya yi fice wajen fallasa ciki da wajen ayyukan ta’addanci a gabashin Sakkwato da Zam-fara ya bayyana cewa ƙarfin bindiga kawai zai sa Turji ya ajiye makamai amma ba ta hanyar sulhu ba.
- Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa
- Askarawan Zamfara Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Bindiga, Kacalla Ɗanbokolo Ubangidan Turji
Ya ce, “Ƙasarmu guda, yankinmu guda, gidanmu guda da Bello Turji don haka muna sane da duk abin da yake yi, idan ya ajiye makamai, to wa ya baiwa kuma kan wani sharaɗi ya ajiye makamai?,” in ji shi.
Guyawa ya bayyana cewa Sheikh Musa Assadus- Sunna da ya ce Turji ya ajiye makamai ba gaskiya ba ne, ya dai ga ɗan bindigan kuma ya ba da labarin ganin sa, ya ce idan har Sheikh Ahmad Gummi da yake babban malami mai kima da martaba zai kasa jagorantar sulhun, to shi ma ba zai iya ba.
Matashin wanda ya ɗauki shekaru yana fafatukar ganin an kawo ƙarshen matsalolin tsaro a gabascin Sakkwato tare da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri, ya ce ba a taɓa yin sulhu kuma a ci gaba da cin zarafin jama’a ba.
“Shin an taɓa yin sulhu a na cin zarafin jama’a, an taɓa yin sulhu a na sa manoma noman dole, an taɓa yin sulhu a na karbar harajin dole, an taɓa yin sulhu ba a ajiye makamai ba?”
Ya ce Turji da sauran ‘yan bindigansa irin su Kachalla Choma da Kachalla Haru ba za su ajiye makami ba, ya ce suna da kwamandoji da makaman da sun fi a kirga.
Guyawa ya bayyana cewa Malamin bai san Turji ba, bai kuma san yankinsu ba, ya ce su da suke a yankin sun tabbatar Turji bai ajiye makami ba, kuma bai yi sulhu da kowa ba.
Ya ce a kwanan baya Turji ya kashe jami’an tsaro tare da ƙone motarsu, don haka idan ya yi sulhu ba zai yi hakan ba.