Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai (UEFA) ta kama ‘yan wasan Barcelona guda biyu, Lamine Yamal da Robert Lewandowski da laifin karya dokar hana shan ƙwayar ƙara kuzari kafin wasan kusa da na ƙarshe da suka buga da Inter Milan.
A cewar rahoton, UEFA ta ce ‘yan wasan sun kasa bayyana cikakkun bayanai na gwajin da ake yi don gano masu shan irin waɗannan ƙwayoyi.
- Mu Tuna Da Jinin Da Aka Zubar Don Kiyaye Hasken Da Muke Da Shi Yanzu
- Ba Gaskiya Ba Ne Rahoton Da Ke Cewa An Yi Sulhu Da Bello Turji – Guyawa Isa
Saboda haka, UEFA ta ci kowannensu tarar Yuro 5,000, sannan an dakatar da su daga buga wasan farko na Champions League a baɗi.
Haka kuma, kocin Barcelona Hansi Flick, shi ma an shi ci tarar Yuro 20,000, kuma an dakatar da shi daga wasa guda ɗaya saboda saɓa ƙa’idojin ladabi.
Ƙungiyar Barcelona gaba ɗaya za ta biya tarar Yuro 5,250.
Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai.
Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta.
Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp