Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da batan wasu 33.
Shugaba Xi Jinping na bada muhimmanci sosai ga yanayin ibtila’i da mamakon ruwan sama ya haifar a wasu yankuna ciki har da gundumar Yuzhong na Lanzhou, babban birnin lardin Gansu.
Cikin umarnin da ya bayar, Xi Jinping ya ce aiki na gaggawa shi ne yin dukkan mai yuwuwa wajen bincike da ceton mutanen da suka bata da ganowa da sake tsugunar da wadanda ke cikin hadari da rage hadari da dawo da hanyoyin sadarwa da na sufuri nan bada jimawa ba.
Ya ce la’akari da tsanantar yanayi a baya baya nan, ya zama wajibi hukumomin yankuna da sassan gwamnati masu ruwa da tsaki su karfafa aikin hasashen barazana da gargadin wuri, da nema da gano hadduran dake boye da karfafa ayyukan agaji da tsare-tsaren shirin ko-ta-kwana da karfafa daukan matakan takaita aukuwar ambaliya da na bayar da agaji, ta yadda za a tabbatar da tsaron rayukan jama’a a lokaci na damina. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp