Gwamnatin kasar Sin ta mika sabon kason tallafin abinci ga Zimbabwe, a wani mataki na bunkasa ikon kasar na samar da isasshen abinci ga al’ummarta, bayan matsanancin tasirin yanayin El-Nino da ya haifar da fari a shekarar bara.
Yayin bikin mika kayan abincin a jiya Alhamis, wanda aka gudanar a birnin Harare fadar mulkin Zimbabwe, mataimakiyar ministan ma’aikatar kyautata rayuwa, kwadago da walwalar al’umma a kasar Mercy Dinha, ta jinjinawa tallafin na Sin, wanda ya kunshi kimanin tan 3,000 na shinkafa da alkama, kayan da ta ce za su taimakawa ‘yan kasar mafiya fama da kunci.
A nasa bangare kuwa, jakadan Sin a Zimbabwe Zhou Ding, ya jaddada aniyar kasar Sin ta taimakawa Zimbabwe, wajen cimma nasarar wadatar da al’umma da abinci da rage talauci, yana mai cewa, tallafin bangare ne na amsa kiran Zimbabwe ga kasashen duniya, na samar mata da tallafin abinci, biyowa bayan fari da ya daidaita wasu sassan kasar.
Jakada Zhou Ding, ya ce har kullum Sin na dora muhimmancin gaske ga ayyukan samar da abinci da rage fatara. Ya kuma yi fatan kasashen biyu za su ci gaba da karfafa kawance don bunkasa samar da isasshen abinci ga al’umma. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp