Kasar Sin ta gudanar da gwajin farko na gagarumin bikin murnar cika shekaru 80, da cimma nasarar yakin kin jinin harin dakarun Japan, da yakin duniya na biyu da safiyar yau Lahadi a nan birnin Beijing.
Sashen watsa bayarai na shirin bikin, ya ce an gudanar da gwajin kasaitaccen bikin ne tun daga tsakar daren ranar Asabar zuwa wayewar garin yau Lahadin nan, a filin taruwar jama’a na Tian’anmen, gwajin da ya kunshi mahalarta kusan 22,000, da suka hada da ainihin masu shiga bikin, da kuma jami’ai masu tallafawa ayyukan bikin.
Mashirya bikin sun ce, gwajin ya kunshi tabbatar da tafiyar da taron jama’a, da tsarin gudanar da bikin, da kula da kayayyakin aiki, da gudanar jerin abubuwan da za a aiwatar yadda ya kamata.
An tsara gudanar da faretin soji, cikin bikin da zai wakana da safiyar ranar 3 ga watan Satumba mai zuwa, a filin Tian’anmen dake tsakiyar birnin Beijing. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp