Kungiyar Kwadago da ta ‘yan kasuwa ta Nijeriya (NLC da TUC) reshen jihar Taraba sun bayyana shirin fara yajin aiki tun daga karfe 12 na daren Litinin 11 ga watan Agusta, 2025.
Wannan mataki ya biyo bayan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jihar da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
A cikin sanarwar da LEADERSHIP ta samu a daren Lahadi mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar NLC, Adamu-Buba, da sakatariyar kungiyar TUC, Polina Gani, sun yi kira ga mambobinsu da su ba da hadin kai ga matakin da kungiyoyin suka dauka domin neman hakkokinsu a wurin gwamnatin jihar ta Taraba.
Kungiyar kwadagon ta ce, taron ya sake duba wa’adin da aka bayar tun da farko ga gwamnati game da “ayyukan kwamitin tattara bayanan ma’aikata a na’ura ta hanyar amfani da yatsu da kuma rahoton da kwamitin ya bayar”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp