Gwamnatin jihar Kano ta bayyana a ranar Talata cewa, ta bayar da kwangilar gina tituna acikin birnin Kano guda 17 a kan kudi sama da Naira biliyan 40.8.
Titunan ana aikinsu ne a kananan hukumomin Gwale, Nasarawa, Kumbotso, Fagge, Kano Municipal, Tarauni, Dala, da Ungogo.
- Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 14 Sun Yi Bikin Murnar Karɓar Kyautar N23m Daga Bankin STANBIC IBTC
Kwamishinan yada labarai, Ibrahim Waiya ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke rangadi da shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa, a titunan da aka kammala da wadanda kuma ake kan aikinsu.
Waiya ya ce, kwangilolin sun nuna aniyar Gwamna Abba Yusuf na samar da ababen more rayuwa musamman tituna, wanda ya bayyana a matsayin jigon alkawarin da ya yi a yayin yakin neman zabe.
A cewar kwamishinan, ayyukan na da nufin inganta hanyoyin zirga-zirga, da rage cunkoson ababen hawa, da inganta rayuwar al’ummar jihar baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp