Shugaban Rundunar Sojojin Sama (CAS), Air Marshal Hasan Bala Abubakar, ya ce hare-haren da sojojin saman Nijeriya suka kai a yankin Arewa maso Gabas sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 592 tare da lalata kayayyakin yaki 372 na ‘yan ta’adda cikin watanni takwas.
CAS ya bayyana hakan ne a birnin Maiduguri na jihar Borno a ranar Talata yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Babagana Zulum.
- Jiragen Saman NAF Sun Kai Hari Kan Taron ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara
- Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Kwangilar Hanyoyi 17 Akan Naira Biliyan 40.8
CAS, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NAF, Air Cadre Ehimen Ejodame, ya fitar, ya ce rundunar ta aiwatar da hare-hare 798, tare da lalata motocin ‘yan ta’adda 206 da kuma maboyarsu 166 a yankin Arewa maso Gabas.
Ejodame ya rahoto CAS, yana cewa “Tare da ingantattun jirage da ke da ingantattun tsare-tsaren kai hare-hare na dare, jirgin NAF ya kai hare-hare guda 798”.
A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya yabawa NAF bisa ci gaba da bayar da tallafi ta sama wajen gurgunta karfin ‘yan ta’adda da kuma kare al’umma.