Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana a yau Talata 12 ga wata cewa, bisa dokoki ko ka’idojin da suka shafi saka wasu sassa cikin wadanda aka sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, ma’aikatar ta fitar da sanarwa mai lamba 21 da ta 22 a ranar 4 da kuma ranar 9 ga watan Afrilun bana, inda ta saka wasu sassa 28 na Amurka cikin wadanda ta sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, wato hana sayar musu kayayyakin amfanin jama’a da ake iya amfani da su a bangaren soja. Har wa yau, domin tabbatar da matsayar da aka cimma a wajen shawarwarin manyan jami’an Sin da Amurka a bangaren tattalin arziki da cinikayya, an yanke shawarar cewa, tun daga yau Talata 12 ga watan Agusta, za a ci gaba da dakatar da wannan mataki na tsawon kwanaki 90 ga sassa guda 16 na Amurka da Sin ta sanyawa takunkumin bisa sanarwar ranar 4 ga watan Afrilun bana. Sa’annan ga sassan Amurka 12 da Sin ta sanyawa takunkumin bisa sanarwar ranar 9 ga watan Afrilu, za a daina aiwatar da matakin a kan su.
Jami’in ma’aikatar cinikayya ta Sin ya yi karin haske cewa, idan ’yan kasuwa na bukatar fitar da kayayyaki zuwa ga wadannan sassan Amurka, ya kamata su nemi izini daga ma’aikatar cinikayya ta Sin, wadda za ta binciki batun bisa dokoki da ka’idoji, sannan a ba wadanda suka dace izini. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp