Ma’aikatar kudi ta kasar Sin da ma’aikatar ayyukan gaggawa ta kasar, sun ware kudin Sin yuan miliyan 170, kimanin dalar Amurka miliyan 23.8, domin tallafawa ayyukan jin kai ga yankuna bakwai masu matsayin lardi da suka fuskanci ibtila’in ambaliyar ruwa.
Tun daga ranar Asabar 9 ga watan nan, yankuna irinsu Sichuan, da birnin Chongqing a kudu maso yammacin kasar, da lardunan Jiangsu da Anhui a gabashin kasar, sun gamu da saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda ya haifar da ambaliyar ruwa da zaizayewar duwatsu da dai sauransu.
A cewar ma’aikatun biyu, za a yi amfani da kudaden ne wajen tallafawa lardunan Jiangsu, da Anhui, da Hubei, da birnin Chongqing, da lardin Sichuan, da Guizhou a shiyyar kudu maso yammacin kasar, da kuma lardin Gansu na arewa maso yammaci, ta fuskar ayyukan gaggawa na ceton rayukan jama’a, da samar da saukin ibtila’in, ciki har da ayyukan lalubowa, da sake tsugunar da wadanda suka rasa matsugunansu, da tantancewa, da aiwatar da matakan gaggawa masu nasaba da hadurra da su kan biyo bayan ambaliyar ruwa, da gyara gidajen da suka lalace. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp