Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na goyon bayan duk wasu matakai masu dacewa na warware rikicin Ukraine ta hanyar lumana, tana kuma farin ciki da yadda Rasha da Amurka ke ci gaba da tattaunawa, da inganta alakarsu, da ingiza matakan warware rikicin Ukraine ta hanyar bin matakan siyasa.
Lin, ya bayyana hakan ne a Talatar nan, lokacin da aka nemi ya yi tsokaci game da rahoton dake cewa, shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, za su gana a ranar Juma’a 15 ga watan nan domin tattauna batun na Ukraine. Ko da yake dai ba a gayyaci shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, da wakilan kungiyar Tarayyar Turai zaman shawarwarin ba.
Lin ya ce, “Muna fatan dukkanin sassan da batun ya shafa, da masu ruwa da tsaki, za su shiga a dama da su yayin shawarwarin, kana za a kai ga gaggauta cimma yarjejeniyar zaman lafiya bisa adalci, mai dorewa, kuma wadda dukkanin sassan za su amince da ita.” (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp