Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.
Tambuwal, an tsare shi ne a jiya Litinin bayan ya amsa gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa kan badakalar fitar da wasu makudan kudade har naira biliyan 189 a lokacin yana gwamnan jihar Sokoto amma an sake shi a yau Talata.
Majiyar EFCC ta ce an bayar da belin Sanata Tambuwal kuma za a bar shi ya bar hedikwatar hukumar da zarar an cika sharuddan belin sa.
A halin da ake ciki, EFCC ta yi Allah wadai da jam’iyyar ADC bisa zargin sanya siyasa a binciken da ta gudanar kan Tambuwal.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp