An labarta yayin taron watsa labarai game da “Sakamakon da yankin Xinjiang na kasar Sin ya samu cikin shekaru goma da suka gabata” a safiyar yau Asabar cewa, gwamnatin yankin Xinjiang tana kara mai da hankali kan aikin da take gudanarwa a kauyuka bayan da aka cimma burin kawar da talauci, kuma nan gaba za ta ci gaba da kokarin farfado da kauyukan yankin daga fannoni biyar wato sana’o’in kauyuka, da kwararru, da al’adu, da hallitu masu rai da marasa rai da kuma kungiyoyin JKS, ta yadda za a cimma burin farfado da kauyukan dake fadin yankin.
A halin da ake ciki, ana aiwatar da tsarin samar da tallafi da sa ido domin hana sake shiga mawuyancin yanayi a fadin yankin Xinjiang, a sa’i daya, an fitar da manufofin da abin ya shafa domin ci gaba da samar da tallafi ga masu bukata a fannonin ba da ilmi, da kiwon lafiya, da gidaje da sauransu.
Ya zuwa karshen watan Yulin bana, adadin mutanen da aka fitar da su daga kangin talauci wadanda suka samu guraben ayyukan yi a fadin yankin ya kai miliyan 1 da dubu 86, kuma adadin kudin shigar kowanne manomin da aka fitar daga kangin talauci a yankin, ya kai kudin Sin yuan 14,798 a shekarar 2021, adadin da ya karu da kaso 19.55 bisa dari idan aka kwatanta shi da na shekarar 2020. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)