Yar uwa shin kin san amfani da maganin da tafarnuwa ke yi a jikin mace kuwa?
Duk ‘ya mace tana bukatar sanin wannan domin yana da mukukar amfani. Bincike ya nuna cewa mata da yawa suna fama da ciwon sanyi (infection), kaikayin gaba da kuma warin gaba. Shi ya sa hakan yake hana su sukuni kuma suke neme-nemen magunguna ko sabulai (baginal wash) domin kawar da wannan ciwon ko warin gaban.
- Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu
- Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”
Meke kawo ciwon sanyi ga mace akwai dalilai masu yawa da ke kawo wa mace ciwon sanyi amma ga kadan daga cikinsu:
Mata masu biye-biyen maza. An fi yada ciwon ta hanyar jima’i don haka mace ko namiji za su iya harbin wadanda ba su da shi cushe-cushe da shafe-shafen magunguna da mata suke yi da sunan matsi ko karin ni’ima na iya kawo musu kurarraje (rashes), kaikayi (itches), da warin gaba wanda zai rikede ya zama ciwon sanyi.
Amfanin Tafarnuwa:
Tafarnuwa tana daga cikin tsirrai mafiya amfani wadanda duniya ta dade tana amfani da su. Shi ya sa Larabawa suke yawan amfani da ita.
Tana kashe duk wani infections (toilet infections etc)..
Tana fitar da warin gaba.:
Tana maganin ciwuwwuka da dama.
Masu ciki na amfani da ita kafin cikin ya tsufa.
Tana kara ni’ima kuma babbar jagorace wajen samun karfin jima’i da dadewa
Za ki iya amfani da ita lokacin al’ada yayin da jini ya ke daukewa ko yana yi miki wasa.
Yadda za ki hada maganin ciwon sanyi da tafarnuwa:
Ki samu tafarnuwa ki daka ta ki ciri ruwn jikinta ki zubar da tukan. sai ki debi ruwan tafarnuwan kadan ki goga a jikin pad (abin da kike sawa in kina al’ada). Sai ki kawo man zaitun shima ki diga sai ki saka a jikinki ki ci gaba da harkokinki.
Bayan kin saka za ki ji zafi amma ki bari kar ki cire. An fi so ki yi idan za ki kwanta bacci da safe sai ki cire don ya fi shiga jiki. Ana son idan mace za ta yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya kusance ta, da safe sai ta tafasa garin hulba, sai ya huce sai ta zauna a ciki za ta yi hakan har tsawon kwanakin da za ki ji kin daina jin kaikayi ko hamamin warin gaban. Allah ya taimaka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp