Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata9o.
A yau shafin namu zai zo muku da yadda ake tuwan dawa:
- CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD
- Kuri’ar Jin Ra’ayi Ta CGTN: Ya Kamata Japan Ta Martaba Tarihi
Da farko uwargida za ki samu dawarki ki gyara ta sannan ki wanke sai ki shanya ta ta bushe sannan ki kai nika a yi miki mai laushi sai ki tankade, sannan ki dora ruwa a tukunyar da za ki yi tuwan. Idan ruwan ya tafasa sai ki dauko wannan tsakin da kika tankade ba mai laushin ba ki yi talge da sh, sai ki bar shi ya yi ta dahuwa, bayan ya dahu sai ki dauko wannan garin mai laushin ki tuka har sai ya yi daidai kaurin yadda kike so. Daga nan sai ki rufe ki bar shi ya sulala, wato ya dahu sosai daga nan sai ki rage masa wuta ki tuka ki kwashe shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp