Rundunar sojin Nijeriya a ranar Asabar ta kori sojoji biyu – John Gabriel da Gideon Adamu – wadanda ke da hannu wajen kashe fitaccen malamin addinin Islama na Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.
An sanar da korar sojojin ne a wani taron da aka gudanar a bataliya ta 241 RECCE da ke Nguru, inda sojojin ke aiki.
- Kisan Gillar Sheikh Goni Aisami Gashuwa: Asalin Abin Da Ya Faru
- An Shiga Alhinin Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Sheikh Goni Aisami Gashuwa, A Yobe
Gabriel ya amsa laifin kashe Sheikh Aisami a ranar 19 ga watan Agustan 2022 yayin da yake kokarin sace motarsa. Bayan Malamin ya rage masa hanya daga wani shingen binciken sojoji inda ya ke.
Babban kwamandan riko na 241 RECCE Battalion I O Sabo, Laftanar Kanar, ya shaida wa manema labarai cewa, matakin da sojojin suka dauka.
Sabo, Ya kara da cewa hedkwatar sashin II za su mika sojojin ga ‘yan sanda a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, domin gurfanar da sojojin a gaban kotu.