A ranar 19 ga watan Agusta agogon kasar Kenya ne aka gudanar da bikin cudanyar al’adu mai taken “Sautin zaman lafiya” na kasar wanda rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya shirya a Nairobi.
Daraktan CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo inda ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japanawa da kuma yaki da mulkin danniya a duniya. Tuna tarihi shi ne mabudin tabbatar da zaman lafiya, da kare gaskiya da adalci, da kuma samar da makoma mai kyau.
Ya kara da cewa, wannan bikin zai baje kolin fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kasar Sin da dama wadanda ke nuna tarihin yaki da mulkin danniya a duniya. Mun yi imanin cewa kowa zai iya fahimtar kimar zaman lafiya daga shirye-shiryen na bidiyo, da kuma hada kai wajen sauke nauyin kiyaye zaman lafiya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp