Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) a ranar Alhamis ta kori karin wasu ‘yan kasashen waje 51 da wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta yankewa hukuncin ta’addanci da zamba ta intanet.
Mutanen kasashen waje da aka yanke wa hukuncin na daga cikin ‘yan kasar China da Philippines su 192 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta kama a watan Disambar 2024.
‘Yan kasashen waje da aka mayar zuwa kasashen su sun hada da ‘yan China 50 da dan Tunisiya daya.
Wannan ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa kasashensu su 102 a ci gaba da yanke hukuncin da aka fara a ranar Juma’a, 15 ga Agusta, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp