Da safiyar yau Alhamis, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci bikin murnar cika shekaru 60 da kafuwar jihar Xizang mai cin gashin kanta, a dandalin Potala Palace na birnin Lhasa. Mutane kusan 20,000 daga dukkan kabilu da sassa na Xizang ne suka yi murna sosai na tunawa da wannan gagarumar rana.
A wajen bikin, Wang Huning, zaunannen memba a kwamitin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS, kana shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin CPPCC, kuma shugaban tawagar kwamitin tsakiyar JKS, ya ba da kyautar girmamawa da shugaba Xi ya rubuta, mai taken: “Mu gina al’ummar Sin tare, mu rubuta sabon labari mai kyau na jihar Xizang”.
A jawabin da ya gabatar, Wang Huning ya ce, dole ne a bude wani sabon babi mu daidaita harkokin Xizang bisa manufar mulkin Xizang da kwamitin kolin JKS ya tsara bisa halin da ake ciki a sabon zamani, kuma a yi kokarin gina yankin Xizang mai bin salon gurguzu, kuma mai hadin kan al’umma da wadata da wayewa da zaman lafiya.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp