Yawan wutar lantarkin da ake amfani da ita a kasar Sin da ke zama wani muhimmin ma’aunin aikace-aikacen tattalin arziki, ya zarce adadin sa’o’i na kilowatt tiriliyan daya a watan Yuli, kamar yadda hukumar kula da makamashi ta kasar ta bayyana a yau Alhamis.
Wutar lantarkin da ake amfani da ita ta kai adadin kilowatt tiriliyan 1.02 a cikin watan Yuli, wadda ke nuna an samu karuwar kashi 8.6 cikin dari a bisa mizanin na makamancin lokacin a bara, sakamakon yanayin zafin da aka ta fama da shi da kuma hada-hadar ayyukan masana’antu da ake ci gaba da yi ba tare da cikas ba.
Daga watan Janairu zuwa Yuli, adadin wutar lantarki da ake amfani da ita a kasar Sin ya karu da kashi 4.5 bisa dari a mizanin shekara-shekara inda ya kai fiye da sa’o’in kilowatt tiriliyan 5.86. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp