Gwamnan jihar Koros Rubas Bassey Otu ya bayyana cewa, Gwamnatinsa za ta yi hadaka da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, domin a zakulo da albarkatun tattalin arzikin da ke a Tashar Jirage Ruwa da ke a garin Kalaba a jihar.
Kazalika Gwamnan ya sanar da cewa, ta hanyar hadakar, jihar za ta kuma amfana wajen bunkasa Tashar Bakassi da ke a jihara.
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Amfani Da Wutar Lantarki A Sin Ya Habaka Sosai A Watan Yuli
Bassey ya sanar da hakan nr a ranar Alhamis a garin na Kalaba a yayin da ya karbi bakuncin tawagar mahukuntan zartarwa na Hukumar NPA a karkashin jagorancin Shugaban mahukuntan Sanata Adedayo Adeyeye, a ziyarar da suka kai wa Gwamnan.
Gwamnan ya kara da cewa, duba da irin albarkatun tattalin arzikin da ke a jihar yin hadakar a tsakanin jihar da kuma Hukumar ta NPA hakan zai sanya jihar ta amfana da kuma kasa baki daya.
“A madadina da kuma daukacin byalummar jihar mu, ina yiwa Shugaban mahukuntan na NPA da sauran tawagarsa maraba da zuwa wannan jihar mussaman kan zabar jihar zuwa wannan ziyarar ta ku ta farko domin kaddamar da taron ku,”.
“Allah ya albarkanci jihar mu da abubuwan da suka yi kama da irin ayyukan da Hukumar NPA ke gudanarwa, a saboda hakan, akwai bukatar mu yi hadaka da Hukumar ta NPA, mussamman domin jihar ta amfana da kuma kasa baki daya,” Inji Gwamnan.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, tattalin arzikin Nijeriya ya shafe shekaru yana fuskantar kalubalen koma baya, mussamman saboda da rashin samun zuba hannun jari.
Ya buga misali da yadda sa’oin Nijeriya kamar irinsu Afirka ta Kudu da Brazil suka yi Nijeriya fintinkau a bangaren hada-hadar kasuwanni, ta hanyar amfani ta Ruwa.
Kazalika, Gwamna Bassey ya jaddada cewa, kara habaka harkokin hada-hadar ta Ruwa, daya kara taimakawa wajen kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Da yake kara yin bayanin kan Tashar Jiragen Ruwan ta Kalaba Gwamnan ya sanar da cewa, Akwai wasu matsaloli da ake fuskanta, su ne, na marsalar yashe hanyoyin Ruwa a tashar ta Kalaba da kuma ta samun cunkoson Jiragen Ruwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp