Jama’a barkanku da wannan rana ta juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na GORON JUMA’A, shafin da yake bawa kowa damar mika sakon gaishe-gaishensa zuwa ga ‘yan’uwa da abokan arziki, na kusa da na nesa, har ma da wadanda aka dade ba a hadu ba.
Kamar kowane mako yau ma shafin na tafe da wasu sakonnin gaishe-gaishen da ku ka aiko mana, inda sakon farko ya fara da cewa;
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Cibiyoyin Bayar Da Lamuni Kan Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci
Sako daga Fiddausi Umar Muhammad Jihar Kaduna:
Ina gaishe da Mamana da Babana, sai kannena Labiba, Nasira, Fati, Maimuna, Khairat, da yayye na; Yaya Muhammad, Yaya Ibrahim, Yaya Maryam, Yaya Abu, Yaya Larai. Sannan malaman makarantarmu na boko da islamiyya, Malama Aisha, Malama Kubra, Malam Isah, Malam Nuhu, Malam Yahaya, Malama Batulu, ai kawayena na boko da na islamiyya kamar su Wasila Sabo, Fatima Muhammad, Hauwa Yunus, Walida Tahir, da dai sauransu. Da fatan sun yi Juma’a lafiya.
Habib Belloti Maigatari Daga Jihar Jigawa:
Ina gaishe da ‘Yan’uwan musulmai na duniya bakidaya, sai matattarar gidana Hajiya Zakiyya (Maman Hibba), sai daya matata Hajiya Hafsatu (Maman Twins) sai amaryata Hajiya Zainab (Maman Mahmah), sai ‘yayana Muhsina, Hibba, Rahmatullah, Hajara (Mahmah), Hassana da Husaina. Sai abokan kasuwa Malam Sa’idu Mai rumfa, Malam Jamilu Kabiru Rabi’u Hadejia, Alhaji Isah Mai Kaji, da fatan sun yi juma’a lafiya.
Sako daga Ummu’aimana daga Jihar Gombe:
Ina gaishe da Mahifana, da fatan Allah ya kara masu lafiya da nisan kwana, sai y’an’uwa, makoftana, dama kawayena irinsu Zahra’u(maman daddy), Bara’atu Saleh, Shafa Liman mai turare, Asiya Muhammad Tayo(maman Shahid), sai Binta Usman,p Jummai, Yahanasu Jabir, Fatima Jafar, Alhaji Abdulkadir Abdullahi, Zakiyya, da fatan sun yi sallar juma’a lafiya.
Abubakar Siddik Aliyu Jihar Kaduna:
Ina gaishe da gabaki daya dangina, kamarsu Malam Baba Yelwa, Kamal Aliyu, Malam Dahiru, Malam Garba, Nura Wada, Umar Isa Aliyu, Dahira Aliyu, Hadiza Aliyu, Haruna Aliyu, Hafsat Aliyu, Hassan, Nusaiba Yahaya, Zaituna Yahaya, ina masu fatan alkhairi da fatan sunyi juma’a lafiya.
Halima Dikko daga Jihar Katsina:
Ina gaishe da mamana da Babana, sai kannen maihaifana Hajiya Lami, Malam Dabo, Malam Kabiru, Kawu Sani, Hajiya Jummai, Hajiya Liti, Kawu Danlami, Hajiy Ladidi, sai yayyena Yaya Salma, Yaya Asabe, Yaya Suleiman, Yaya Rabi. Da fatan sunyi juma’a lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp