Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta ce daga watan Junairu zuwa Yulin bana, darajar abubuwan da Sin ta shigo da su kasar daga kasashe masu karancin ci gaba na Afrika, ta kai dala biliyan 39.66, adadin da ya karu da kaso 10.2 kan na bara.
Kakakin ma’aikatar He Yongqian ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, inda ta ce wani rahoto da asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya fitar a baya bayan nan, ya nuna cewa, karkashin jagorancin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC, hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika ya zama wani muhimmin karfi mai ingiza ci gaban tattalin arziki a nahiyar. Ta ce cinikayya tsakanin bangarorin biyu na bayar da gudunmowar maki kaso 1 zuwa 2 na habakar tattalin arzikin nahiyar a kowacce shekara, kuma jarin kasar Sin ya kara aikin sarrafa kayayyaki a cikin gida na Afrika daga kaso 15 zuwa 45. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp