Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 ga Wadanda ambaliyar ruwa ta shafa ‘yan kasuwar kantin Kwari da ke jihar Kano.
Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa an yi asarar kaya na miliyoyin nairori sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa kasuwar a makon jiya.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani gagarumin liyafar da Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a jam’iyyar, Ibrahim Shekarau ya yi a Kano a ranar Litinin.
A cikin gajeren jawabinsa, Atiku ya jajanta wa ‘yan kasuwar da abin ya shafa kafin ya bayyana tallafin.