LJami’an kasar Senegal, da shugabannin siyasa, da masana, sun bayyana irin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) na birnin Beijing, a wani taron da aka gudanar a ranar Jumma’ar da ta gabata a Dakar, babban birnin kasar ta Senegal.
Ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Senegal ya karbi bakuncin taron a bikin cika shekara guda da fara aiwatar da sakamakon taron, inda ya tattaro mahalarta kusan 100 da suka hada da manyan jami’an gwamnati, da wakilan jam’iyya, da kuma kwararrun masana.
Sakatare-janar na jam’iyyar “African Patriots of Senegal for Work, Ethics and Fraternity” da ke mulkin kasar Senegal, Ayib Daffea ya bayyana cewa, kwarewar da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta samu wajen gudanar da harkokin mulki, ta bayar da muhimman darussa ga kasar Senegal wajen lalubo hanyar zamanantarwa da ta dace da yanayin kasar. Ya kara da cewa, jam’iyyarsa a shirye take ta zurfafa mu’amala da kasar Sin, domin kara yaukaka zumunci da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu.
A nata bangaren, darektar kula da yankin Asiya da Fasifik da Gabas ta Tsakiya a ma’aikatar kula da hadin kan Afirka da harkokin wajen kasar Senegal Cathy Diagne Thioye, ta bayyana dandalin FOCAC a matsayin abin koyi a bangaren hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ta yi kira ga bangarorin biyu da su ci gaba da yin aiki tare don aiwatar da muhimman ayyukan da suka sa a gaba a karkashin tsarin dandalin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp