Da misalin karfe 9 na safiyar yau Laraba 3 ga Satumba ne aka gudanar da gagarumin bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun Japan, da kuma yakin duniya na kin tafarkin murdiya a filin Tian’anmen na birnin Beijing bisa jigon “Tunawa da tarihi, girmama jarumai, martaba zaman lafiya da kuma samar da ci gaba”, inda aka yi gagarumin bikin faretin sojoji, tare da al’ummomin duniya don tunawa da wannan rana mai girma.
Cikin sautin wakar soja mai karfi, Xi Jinping dake tsaye cikin wata mota ya bi faffadan titin Chang’an ya duba faretin rundunonin sojoji, da na kayayyakin soja dake jere.
Yayin wannan biki, akwai rundunoni 45 (da jirage) da aka duba, kuma da farko an duba faretin rundunonin sojoji 13 dake fareti da kafa. Sojojin al’ummar Sinawa sun cimma sabon tsari bayan da aka yi musu kwaskwarima, inda a karon farko aka gabatar da nau’o’in sojoji 4, wato sojin kasa, da sama, da ruwa da roka, da rundunonin sojoji 4, wato sojojin sararin sama, da na yanar gizo, da na tallafin bayanai, da kuma sojoji masu ba da hidima. Ban da wannan kuma, dukkan rundunonin soja da yan sandan tsaron cikin gida, sun rike tutocinsu a wannan biki.
Bisa goron gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi musu, shugabanni 26 na kasashe da na gwamnatocin ketare sun halarci bikin. Sannan wasu shugabannin majalisun dokokin kasashe, da mataimakan firaministocin wasu kasashe, da manyan wakilai, da shugabannin hukumomin kasa da kasa, da tsoffin shugabannin siyasa na kasashe da dama su ma sun halarci bikin.
Ban da wannan kuma, an gayyaci jakadun ofisoshin jakadanci na kasashen waje dake kasar Sin, da jami’an ofishin jakadanci dake kula da harkokin soji, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa dake zaune a kasar Sin, da abokai 50 da iyalansu daga kasashe 14 da suka hada da Rasha, da Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da kuma Kanada.
Shekaru 80 da suka gabata, al’ummar kasar Sin sun samu gagarumar nasara a yakin kin hare-haren sojojin Japan bayan shekaru 14 masu cike da wahalhalu, tare da bayyana cikakkiyar nasarar yaki da mulkin danniya a duniya. Sin ta fara yakin kin hare-haren ne tun daga farko har karshe a tsawon lokaci, kuma bisa gagarumar sadaukarwar al’ummun Sin, kasar ta bayar da goyon baya a babban fagen yaki na yaki da mulkin danniya a gabashin duniya, tare da ba da muhimmiyar gudummawa ga samun nasarar yaki da mulkin danniya a duniya. (Amina Xu, Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp