Wata jami’ar Asusun ba da lamuni na duniya IMF ta yaba da kwararan bayanan tattalin arzikin kasar Sin da suka nuna samun ci gaba fiye da yadda aka zata a farkon rabin shekarar nan, tare da aiwatar da manufofin kasafin kudi da suka hada da kokarin bunkasa sayayyar kayan masarufi.
Jami’ar wacce take shugabar ofishin IMF na kasar Sin Sonali Jain-Chandra, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, “Wasu daga cikin matakan da aka dauka a cikin kasafin kudin, kamar fadada shirin cinikayya, ina ganin misali ne guda daya da zan bayar, da kuma kokarin ganin kananan matakan gwamnatoci sun biya basussukan da ake binsu, ina ganin wadannan su ne abubuwan da suka haifar da juriyar sayayyar kayan masarufi da muka gani a farkon rabin shekarar.”
Jain-Chandra ta kara da cewa, bangaren masana’antu na kasar Sin shi ma ya nuna kwazo sosai, bisa karfin ayyukan manyan masana’antu irin nasu motoci da na’urorin lantarki, wanda ya samu ci gaba da abin da ya kai kaso 10 zuwa sama a shekarar 2025.
Jami’ar ta IMF ta ce, a yanayin da ake ciki na rashin kwanciyar hankali a bangaren kasuwanci a halin yanzu, ya kamata kasashe su nemi yadda za a rage rashin tabbas da manufofi suka haifar ta hanyar inganta tsare-tsaren kasuwanci masu adalci.
“Wannan kuwa ya hada da bin hanyoyin amfani da tsare-tsare na mabambantan bangarori game da alkiblar kasashen duniya ta bai-daya, da zamanantar da ka’idojin kasuwanci a duk inda ya dace, da kuma neman hanyoyin warware al’amuran da suka cude daga bangarori daban daban ko kuma a mataki na yanki,” kamar yadda jami’ar ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp