A cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, bisa gayyatar da shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron koli na shugabannin kasashen kungiyar BRICS da za a yi ta kafar bidiyo, daga nan birnin Beijing a gobe Litinin, tare da gabatar da muhimmin jawabi.(Safiyah Ma)














