A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron kungiyar BRICS ta yanar gizo daga nan birnin Beijing, inda ya gabatar da muhimmin jawabi.
Cikin jawabin na sa, shugaba Xi ya ce wata kasa ta kaddamar da jerin matakai na yakin cinikayya da na haraji, matakin da ya yi matukar illata tattalin arzikin duniya. Ya ce a wannan muhimmiyar gaba, a matsayinsu na jagororin gungun kasashe masu tasowa, ya wajaba kasashe membobin kungiyar BRICS su rungumi ruhin yin komai a bude, da game dukkanin sassa, da cimma nasarar hadin gwiwar moriyar juna, da kuma aiki tare wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga bil’adama.
Shugaban na Sin, ya kuma gabatar da shawarwari guda uku, wadanda suka hada da na farko martaba cudanyar mabanbantan sassa da kare gaskiya da adalci. Na biyu kuma a rungumi akidar yin komai a bude da cimma nasarar hadin gwiwar moriyar juna, da wanzar da tsarin gudanar da hada-hadar tattalin arziki da cinikayya. Sai kuma shawara ta uku, wato nacewa hadin kai da hadin gwiwa, da dunkule karfin sassa daban daban domin cimma nasarar bai daya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp