Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin sufurin kasa ya bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga Ministan Sufuri, Sa’idu Alkali da ya gurfana a gabanta kan yadda jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsari wanda ke ɗauke da fasinjoji 618 a kwanakin baya.
Kwamitin ya ɗau matakin ne a ranar Talata, biyo bayan gazawar da ministan ya yi na gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi kan lamarin.
- Kasar Sin Ta Zama Dandalin Karfafa Cudanya Da Cinikayya Tsakanin Kasa Da Kasa
- Nazarin CGTN: Cin Gajiyar Damarmaki Tare Da Samun Sakamakon Moriyar Juna Ta Hanyar Yin Komai A Bude
Shugaban kwamitin, Hon. Blessing Onuh wacce ta nuna rashin jin daɗinta kan rashin zuwan Alkali, ta ce ba za a amince da wannan ɗabi’a ba, “juya wa ‘yan Nijeriya baya a lokacin da suka fi bukatarsa ba.”
Onuh ta ce, “Ba zai yi wu ba, mu bar ayyukanmu, da yawa daga cikinmu sun yanke hutun da suke kai, muka taho daga Legas saboda wannan zama amma Ministan ya yi watsi da kiran majalisar.
“An jefa ‘yan’uwanmu cikin hatsari, wannan ba abun wasa ba ne, don haka mun dakatar da taron kuma mun umarci Ministan ya bayyana a gaban wannan kwamitin cikin sa’o’i 48.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp