Kasar Sin ta fitar da wani mizani na kididdige cinikayya tsakaninta da sauran kasashe mambobin kungiyar BRICS jiya Talata, a wajen bikin baje kolin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa karo na 25 na kasar, da ake yi a birnin Xiamen na lardin Fujian da ke gabashin kasar ta Sin. Mizanin da aka fitar a Xiamen ya nuna an samu dorewar ci gaba duka a bangaren ma’aunin cinikayya da kuma tsarin da aka yi.
Wanda Babbar Hukumar Kwastam (GAC) ta tattara bayanansa, mizanin ya fara aiki ne a shekarar 2009, shekarar da shugabannin BRICS suka gudanar da taronsu na farko, tare da darajar maki 100. A cikin shekarar 2024 kuma, mizanin ya haura zuwa darajar maki 301.51.
Mizanin ya kunshi alamomi ko ma’aunai guda hudu wadanda ke auna kididdiga, da tsari, da sabbin kirkire-kirkire da kuma kwazon iya cinikayya. An tsara shi ne don sa ido kan ci gaban kasuwanci tsakanin bangarorin biyu da taimakawa wajen yanke shawara ga sassan gwamnati da kuma kamfanoni.
Daga shekarar 2009 zuwa 2024, wadannan alamomi ko ma’aunai guda hudu sun nuna samun ci gaba mai inganci, inda darajar makin cinikayya ta kai 283.73, darajar makin tsarin da aka yi ta kai 192.27, ta kirkire-kirkiren kasuwanci ta kai 342.81, kana ta kwazon iya cinikayya ta kai maki 387.21, wadanda ke nuna samun karin kuzarin cinikayya tsakanin Sin da sauran mambobin BRICS. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp